• (Harshen Turanci) -"Akwai ƙishirwa a cikin zukatanmu a gare ku, Ya Ubangiji".3gp
    Apr 15 2022
    (English Version)"There is a Longing in Our Hearts for You, Oh! Lord".3gp
    Más Menos
    3 m
  • Harshen Hausa(هَوُسَ)- "Gayyatar Sanin Yesu Da Kansa".3gp
    Apr 15 2022
     Hausa(هَوُسَ)- "Invitation to Know Jesus Personally(English)".3gp
    Más Menos
    6 m
  • Wakar Bautar Hausa Mai Karfi.3gp
    Apr 15 2022
    Powerful Hausa Worship Song.3gp // 1KOR 15. - Tashin Almasihu daga Matattu1A yanzu kuma, 'yan'uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi, 2wadda kuma ake cetonku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama sama ne kuka gaskata ba. 3 Ish 53.5-12 Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa, 4Zab 16.8-10; Mat 12.40; A.M 2.24-32 cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa, 5Luk 24.34; Mat 28.16,17; Mar 16.14; Luk 24.36; Yah 20.19 ya kuma bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun. 6Sa'an nan ya bayyana ga 'yan'uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda, yawancinsu kuwa suna nan har zuwa yanzu, amma waɗansu sun yi barci. 7Sa'an nan ya bayyana ga Yakubu, sa'an nan ga dukan manzanni. 8A.M 9.3-6 Daga ƙarshen duka ya bayyana a gare ni, ni ma da nake kasasshe, marar cancanta. 9A.M 8.3 Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikkilisiyar Allah. 10Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata. 11To, ko ni ne dai, ko kuma su ne, haka muke wa'azi, ta haka kuma kuka gaskata.
    Más Menos
    2 m
  • Hausa Kirista Wakar Waka.3gp
    Apr 15 2022
    Hausa Christian Hymn Song.3gp
    Más Menos
    3 m
  • Harshen Hausa - "Hanyoyi Biyu".mp3
    Apr 15 2022
    Hausa Language - "The Two Roads(English)".mp3 // YAH 1. - Kalman Ya Zama Mutum1Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. 4Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba. 6Mat 3.1; Mar 1.4; Luk 3.1,2 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken. 9Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah. 14Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa. 15Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ” 16Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri. 17Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. 18Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.
    Más Menos
    1 m
  • Harshen Hausa(حَوْسَ) - " Yayi kyau Labarai".3gp
    Apr 15 2022
    Hausa(حَوْسَ)  Language - "Good News(English)".3gp
    Más Menos
    4 m
  • Hausa(حَوْسَ ) - "Yesu: Ubangiji & Mai Ceto".3gp
    Apr 15 2022
    Hausa(حَوْسَ ) - "Jesus: Lord & Saviour(English)".3gp // 1KOR 13. - Ƙauna1Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala'iku, amma ya zamana ba ni da ƙauna, na zama ƙararrawa mai yawan ƙara ke nan, ko kuwa kuge mai amo. 2 Mat 17.20; 21.21; Mar 11.23 Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne. 3Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in har ba ni da ƙauna, to, ban amfana da kome ba. 4 Ƙauna tana sa haƙuri da kirki. Ƙauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. 5Ƙauna ba ta sa ɗaga kai ko rashin kārā, ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo. 6Ƙauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. 7Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali. 8 Ƙauna ba ta ƙarewa har abada. Annabci zai shuɗe, harsuna za su ɓace, ilimi kuma zai shafe. 9Ai, hakika iliminmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. 10Sa'ad da kuwa cikakken ya zo, sai ɗan kiman nan yă shuɗe. 11Sa'ad da nake yaro, nakan yi magana irin ta ƙuruciya, nakan yi tunani irin na ƙuruciya, nakan ba da hujjojina irin na ƙuruciya. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin ƙuruciya. 12Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai. 13To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, da bege, da kuma ƙauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
    Más Menos
    1 h y 28 m
  • Hausa(حَوْسَ) - "Yesu: Malami kuma Mai warkarwa".3gp
    Apr 15 2022
     Hausa(حَوْسَ) "Jesus: Teacher and Healer(English)".3gp
    Más Menos
    43 m