• Kashi na 43 – Shiri na musamman
    Nov 17 2015
    Yanzu an kusan shawo kan matsalar hasken fitilar nan. Sai dai kuma Paula da Philipp ba su ji dadi ba, domin kuwa ga labarin nan duk ya fito a cikin jarida. Ko a ina abokan hamayyarsu suka samo labarin? Paula da Philipp sun ga mummunan labari: akwai cikakken labarin wannan filtila mai mugun haske a cikin wata jarida. Wato, saura su bincike dalilin da ya sa ba a tsaron kofar kamfanin sosai. Sai 'yan jaridar suka nufi wurin. Suna fatan in sun kai za su ga ana hira da 'yan jaridu, ko kuma kakakin kamfanin yana bayani. To, wane ne ya yi hira ke nan? Wannan rudanin ya sa shi ma Farfesa ya yi irin wannan tambaya, sannan kuma ya yi bayani a kan jawabi kai-tsaye da kuma a kaikaice.
    Show more Show less
    15 mins
  • Kashi na 42 – Aiki ya samu Eulalia
    Nov 17 2015
    Paula da Philipp sun kusa gano wannan al'amari. Yanzu haka dai sun san daga inda mugun hasken nan yake fitowa. Sai dai kuma Eulalia ba ta dawo daga leken asirin da ta tafi ba. Me ya faru? Bayan Paula da Philipp sun gano daga inda hasken yake fitowa, sun sanar da kamfanin fitilun don a warware matsalar. Amma sun fi damuwa da bacewar Eulalia. Sai kawai 'yan jaridun suka ji wani kuka. Ko wani abu ya samu Eulalia ne? Bayan wannan rintsi da aka shiga, yanzu masu saurare za su dan shakata da nazarin kalmomin nahawu. Farfesan yana bayani a kan wakilan suna na mallaka na mutum na uku, wato "sein" da "ihr".
    Show more Show less
    15 mins
  • Kashi na 41 – Agaji daga sama
    Nov 17 2015
    Wakilan Radio D ba su yi nisa da binciken nasu ba. Sai kawai ga mujiya Eulalia ta bayyana a garin Jena. Watakila za ta iya kawo musu agaji. Paula da Philipp ba za su iya shiga cikin kamfanin fitilun ba saboda ginin na da tsayi. A nan Elulalia take da ranarta tun da za ta iya ganin dakunan binciken kamfanin daga sama. Wannan mujiya mai basira dai ta gano abubuwa da yawa. Amma kuma wani abin ba-zata ya faru. Abubuwan da ke faruwa sun ruda Farfesa ma. Don haka a cikin wannan kashi ya yi bayanin kalmar aikatau mai haska baya, wato "konzentrieren". Wannan wata dama ce ta nazarin wakilan suna masu haska baya.
    Show more Show less
    15 mins
  • Kashi na 40 – Kafar samun labarai
    Nov 17 2015
    Wani abu ya fado a zuciyar Paula da Philipp, shi ya sa ma suke son su san irin abin da kwararru a kan fitilu masu mugun haske ke aikatawa a garin Jena. Tuni ma sun san inda za su samo labarinsu. Paula da Philipp sun je kamfanin fitilun don su yi bincike. Yin hira a wurin zai taimaka musu da amsoshin da suke nema. Sai dai kuma kakakin kamfanin ya kore su, ya ki ya ba su bayanai. Amma sai 'yan jaridun suka gudanar da nasu binciken a asirce kuma suka zama ganau da idonsu. A nan ma dai Farfesa ya nuna shi ya fi kakakin kamfanin karadi, inda ya yi bayanin magana ta yau da kullum, musamman yadda ake takaita maganar baka.
    Show more Show less
    15 mins
  • Kashi na 39 – Ta'addancin fitila mai mugun haske a garin Jena
    Nov 17 2015
    Da isarsu garin Jena, sai Paula da Philipp suka shiga binciken wannan lamari na ta'addancin. Kafin haka ma ashe an sake aikata wannan lamari. To, me yake faruwa haka? A kan hanyarsu ta zuwa otel, 'yan jaridar sun sami damar tambayar direban tasin da suke ciki a kan wannan abin da yake faruwa a gari. Sai ma kuma kawai suka yi kacibus da abin a gabansu: wani yana fasa maduban motocin mutane da fitila mai mugun haske. Ko wannan harin yana da nasaba da taron da aka yi ne yanzu haka a kan fitila mai haske a garin Jena? Yanayin kalmomin nahawu dai a wannan darasi ba su da wahala. Farfesa ya yi bayanin kalmomin wuri da bayanau kamar su "mit", da "zu", da kuma "in" wadanda suke daukar jakada.
    Show more Show less
    15 mins
  • Kashi na 38 – Zuwa garin Jena ta jirgin kasa
    Nov 17 2015
    Tun da motar Philipp ta lalace, sai 'yan jaridar Radio D suka hau jirgin kasa zuwa wurin da za su dauko rahotonsu na gaba, inda abubuwan ban mamaki ke ta faruwa. Wata dama ce ga Paula da Philipp ta bincika al'amura. Yayin da Philipp ya kai motarsa wajen gyara, tuni an fara wani bincken. An sami labarin cewa wani mutum a garin Jena na nan na damun mutane yana haska su da fitila mai mugun haske. Paula da Philipp na da bukatar su leka don su binciki wannan al'amari. Don haka sai suka hau jirgin kasa suka nufi wurin da abin yake faruwa. Sai dai kuma kamar yadda yake faruwa, ba komai ne ke tafiya kamar yadda ya kamata ba. Farfesa ya yi amfani da wannan dama don ya yi bayani a kan kalmar aikatau ta "sollen" idan ta fito a jumlar bayani ko ta tambaya.
    Show more Show less
    15 mins
  • Kashi na 37 – Wasikun masu saurare
    Nov 17 2015
    Yanzu Farfesa zai amsa tambayoyin masu saurare kan darussan da suka gabata. Zai yi amfani da faifan don nuna masu saurare cewa za su iya fahimtar abubuwa da yawa ba tare da sun fahimci kowace kalma da aka furta ba. Wasikun masu saurare sun fi mayar da hankali ne a kan dabarun fahimtar maganar baki. Kamar koyaushe dai, Farfesan ya amsa tambayoyin masu saurare, tare da bayar da shawarwari a kan dabarun saurare da fahimta da kuma sanin kalmomi. Daga cikin abubuwan da ya gabatar akwai yadda ake sanarwa cikin amsa-kuwwa, da yadda ake kira da amsa waya, da kuma yadda ake sanarwa ta rediyo. Haka kuma masu saurare na iya gane abubuwan da ake fada ta yadda ake sauya murya, da kuma ta kalmomin da aka sani, da kuma irin hayaniyar da ake ji a bayan fage. Haka kuma suna iya cankar ma'anar kalmomin da ba su sani ba daga yanayin da ake maganar.
    Show more Show less
    15 mins
  • Kashi na 36 – Labarin Ludwig van Beethoven
    Nov 17 2015
    Ludwig Beethoven ya kirkiro wani shahararren kidan da ake kira "Ode to Joy" yana da shekara 22. Kidan dai ya zamo taken Tarayyar Turai. Wannan kidan da ake ji daga gidan Beethoven shi zai mayar da mu karni na 18. Shi dai Ludwig van Beethoven na daga cikin shahararrun 'yan asalin birnin Bonn. Ga Paula da Philipp nan za su saka mana shahararren kidan nasa mai suna "9th symphony", da kuma irin yadda matsalar kurunta ta afka wa rayuwar wannan shahararren makadi. Idan har mutum bai fahimci abu ba, yana da kyau a maimaita masa. A nan ma Farfesa na bayani ne a kan magana ba ta kai-tsaye ba a cikin sassan jumla ta hanyar amfani da mahadin "dass".
    Show more Show less
    15 mins