• Yadda Sabon Mafi Karancin Albashi Zai Iya Daidaita Al’amura
    Jul 30 2024

    Send us a Text Message.

    Shugabann Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000.

    Yayin da ma’aikata ke ganin za su fara shagali, a gefe guda wasu masu kamfanonin da ‘yan kasuwa na ganin kamar an dora musu nauyin da ya fi karfinsu.

    Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan sauyin da za a iya samu saboda sabon albashin.

    Show more Show less
    18 mins
  • Dalilin Takaddama Kan Rushe Hukumomin Raya Biranen Kaduna
    Jul 26 2024

    Send us a Text Message.

    Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta soke dokar da ta kirkiri hukumomin raya wasu biranen jihar uku.

    Wannan mataki dai ya haifar da zazzafar muhawarar a kan nasabarsa da nuna yatsa da ake yi a tsakanin gwamnati mai ci da wadda ta gada.

    Shirin Najeriya a Yau zai binciki dalilin daukar wannan mataki da yadda zai shafi ci gaban kananan hukumomin da abin ya shafa.



    Show more Show less
    22 mins
  • Shin Zanga-Zanga Na Tasiri A Najeriya?
    Jul 25 2024

    Send us a Text Message.

    A lokuta da dama idan ran ‘yan kasa ya baci su kan dauki matakin nuna fushinsu ga gwamnati ta hanyar zanga-zanga.

    Ana yawan kokwantn shin zanga-zangar da ake gudanarwa a Najeriya suna haifar da ɗa mai ido? Ta wace hanya zanga-zanga ta zama silar samar da maslaha?

    Ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a yau.



    Show more Show less
    22 mins
  • Abin Da Masu Zuba Jari Suke Gudu Daga Najeriya
    Jul 23 2024

    Send us a Text Message.

    Masana na nuna fargaba game da rashin tabbas a harkar zuba jari a Najeriya.

    Tun a watannin da suka gabata ake ta samun ficewar manyan kamfanoni daga kasar, lamarin da ake alakantawa da wasu tsare-tsaren tattalin arziki.

    Shirin Najeriya a yau zai tattauna kan yadda hakan zai ci gaba da tasiri a kan tattalin arzikin Najeriya.



    Show more Show less
    22 mins
  • Alaƙar Da Ke Tsakanin Masu Haƙar Ma’adanai Da ‘Yan Bindiga
    Jul 22 2024

    Send us a Text Message.

    Jihohin Zamfara da Neja a Arewacin Najeriya na cikin jihohin da ke fuskantar kalubalen tsaro duk da tarin ma’adanai da suke da su.

    Sai dai duk da zafin hare-haren da ake samu a wadannan jihohi aikin hakar ma’adanai na ci gaba kamar yadda aka saba.

    Shin wace alaka ke tsakanin masu hakar ma’adanai da ‘yan bindiga? Wani binciken da Daily Trust ta gudanar ya gano haka, kamar yadda za ku ji a cikin shirin Najeriya a Yau.

    Show more Show less
    26 mins
  • ‘Yadda APC Ke Kokarin Rufe Bakin Masu Sukar Gwamnati’
    Jul 19 2024

    Send us a Text Message.

    Ana musayar yawu kan ’yancin ’yan kasa na fadin albarkacin bakinsu game da manufofin gwamnati mai ci.

    ’Yan adawa na zargin jam’iyar APC mai mulki da kokarin rufe bakin masu yi mata gyara a inda ta yi kuskure.

    Shirin Najeriya a yau zai tattauna ne a kan abin da ya sa hakan yake faruwa.

    Show more Show less
    26 mins
  • Me Ya Sa Gwamnoni Ke Rige-Rigen Yin Zaben Kananan Hukumomi?
    Jul 18 2024

    Send us a Text Message.

    Gwamnoni da dama a Najeriya sun bayyana aniyarsu ta gudanar da zabukan kananan hukumomi kafin karshen wannan shekarar.

    Zuwa yanzu jihohi 13 aka lissafa za su gudanar da zabubbukan, lamarin da wasu ke alakantawa da hukuncin Kotun Koli da ya bai wa kananan hukumomin ’yancin cin gashin kai.

    Shirin Najeriya a yau zai yi bincike ne don gano gaskiyar wannan lamari.

    Show more Show less
    22 mins
  • Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Azumin Tasu’a Da Ashura
    Jul 16 2024

    Send us a Text Message.

    A yau ne ake kammala azumin Tasu'a da Ashura, wato na kwanakin Tara da Goma cikin watan farko na kalandar Musulunci da Musulmai ke yi.

    Azumi ne da ake yi cikin watan Muharram, wanda malamai ke cewa yana daya daga cikin watanni hudu mafiya Alfarma a shekarar Musulunci.

    Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake azumin Tasu'a da Ashura da muhimmancin shi ga rayuwar Musulmai.

    Show more Show less
    15 mins