• Abin Da Ke Faruwa Da Bankunan Da Suka Haɗe Waje Guda
    Aug 14 2024

    A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna.

    A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya.

    To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin lamarin na shafar kwastomomi?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi bayani kan abin da ke faruwa a duk lokacin da bankuna suka yi maja a waje da juna.

    Show more Show less
    23 mins
  • Yadda Za Ku Gane Shafukan Tallafin Gwamnati Na Bogi
    Aug 7 2024

    Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma.

    Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan intanet na tallafin gwamnati na bogi da na gaske.

    Show more Show less
    24 mins
  • Abin Da Gwamnati Za Ta Yi Idan Tana Son Hana Zanga-Zanga
    Jul 31 2024

    Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka.

    Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma.

    Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga.

    Show more Show less
    28 mins
  • Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama
    Jul 24 2024

    A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya.

    Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali.

    Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba.

    Show more Show less
    23 mins
  • Ko Tallafin Shinkafar Gwamnati Zai Magance Damuwar Talakan Najeriya?
    Jul 17 2024

    Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi.

    A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri.

    Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuwar talakan Najeriya.

    Show more Show less
    25 mins
  • Matakan Kauce Wa Hadarin Ambaliyar Ruwa
    Jul 10 2024

    Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa.

    A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine.

    Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.

    Show more Show less
    30 mins
  • Digiri Ko Sana’a - Wanne Ya Fi Muhimmanci?
    Jul 3 2024

    Ana ci gaba da tafka muhawara a kan abin da ya kamata mutum ya fi bai wa muhimmanci a tsakanin digiri da sana’a.

    Shin wanne ne daga ciki mafi a'ala a rayuwar mutum?

    Shirin Daga Laraba zai yi muhawara a kan wannan batu.

    Show more Show less
    30 mins
  • Shirin Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Magance Matsalar Tsaro
    Jun 26 2024

    Yayin da ake kammala taron yini biyu a kan matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, hankali ya karkata zuwa ga mataki na gaba.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda gwamnonin yankin suka shirya aiwatar da abin da aka cimma.

    Show more Show less
    23 mins