Episodios

  • Shin Tallafin Abinci Ne Zai Magance Damuwar Talakan Najeriya?
    Jul 17 2024

    Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi.

    A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri.

    Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuwar talakan Najeriya.

    Más Menos
    25 m
  • Matakan Kauce Wa Hadarin Ambaliyar Ruwa
    Jul 10 2024

    Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa.

    A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine.

    Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.

    Más Menos
    30 m
  • Digiri Ko Sana’a - Wanne Ya Fi Muhimmanci?
    Jul 3 2024

    Ana ci gaba da tafka muhawara a kan abin da ya kamata mutum ya fi bai wa muhimmanci a tsakanin digiri da sana’a.

    Shin wanne ne daga ciki mafi a'ala a rayuwar mutum?

    Shirin Daga Laraba zai yi muhawara a kan wannan batu.

    Más Menos
    30 m
  • Shirin Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Magance Matsalar Tsaro
    Jun 26 2024

    Yayin da ake kammala taron yini biyu a kan matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, hankali ya karkata zuwa ga mataki na gaba.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda gwamnonin yankin suka shirya aiwatar da abin da aka cimma.

    Más Menos
    23 m
  • Yadda Kanawa Suka Je Kallon Hawan Daushe A Zazzau
    Jun 19 2024

    Hawan Daushe al’ada ce ta sarakunan Kasar Hausa a lokacin bikin Sallah.

    A masarautar Zazzau a kan yi wannan hawa a ranar ukun Sallah da yamma, kuma yakan tara ‘yan Kallo daga wurare daban-daban ciki har da Kano.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda aka yi hawan na bana da yadda ya samo asali musamman a masarautar Zazzau.

    Más Menos
    29 m
  • ‘Na Yi Nadamar Ajiye Aiki Saboda Tsohon Mijina’
    Jun 12 2024

    Yayin da wasu mazan suke kyale matansu su yi aiki, wasu kan yi kememe su ki bari nasu matan su yi.

    Shin barin matar aure ta yi aiki ne ya fi alheri ko hana ta? Wadanne dalilai kowanensu ke da su?

    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a cikin wannan lamari.

    Más Menos
    25 m
  • Dalilin Da Maza Ba Su Son Likita Namiji Ya Duba Matansu
    Jun 5 2024

    A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci.

    Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su.

    Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.

    Más Menos
    29 m
  • Ƙalubale Da Ci Gaban Dimokraɗiyar Najeriya Cikin Shekara 25
    May 29 2024

    Najeriya ta cika shekara 25 cikin tsarin dimokradiyya ba tare da katsewa ba.

    Ana kan tsari ne na shugaban kasa mai cikakken iko tun daga 1999 a ranar 29 ga watan mayu, duk da yake an sauya bikin wannann rana zuwa 12 ga watan Yuni.

    Toh shin wane irin ci gaba ko akasin haka aka samu cikin wadannan shekaru 25?

    Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna kan wannan cikar Najeriya shekara 25 cikin mulkin dimokradiyya.



    Más Menos
    29 m