Episodios

  • Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Azumin Tasu’a Da Ashura
    Jul 16 2024

    Send us a Text Message.

    A yau ne ake kammala azumin Tasu'a da Ashura, wato na kwanakin Tara da Goma cikin watan farko na kalandar Musulunci da Musulmai ke yi.

    Azumi ne da ake yi cikin watan Muharram, wanda malamai ke cewa yana daya daga cikin watanni hudu mafiya Alfarma a shekarar Musulunci.

    Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake azumin Tasu'a da Ashura da muhimmancin shi ga rayuwar Musulmai.

    Más Menos
    15 m
  • Yadda Matasa Za Su Gina Rayuwarsu Da Ta Al’umma
    Jul 15 2024

    Send us a Text Message.

    Yau ce Ranar Matasa Masu Sana’a ta Duniya.

    A wannan shekarar Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta ayyana wannan rana, tana son a yi amfani da basirar matasa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.

    Shirin Najeriya a Yau zai duba yadda wanann buri zai cika.

    Más Menos
    19 m
  • Wane Sauyi 'Yancin Cin Gashin Kai Zai Kawo A Kananan Hukumomi?
    Jul 12 2024

    Send us a Text Message.

    Hukuncin kotun koli kan ikon kananan hukumomi ya jefa su cikin farin ciki a fadin Najeriya.

    Sai dai yanzu abin da ake son ganin ya faru shi ne yaushe wannan tsari zai yi tasiri kuma me ya rage ga kananan hukumomi.

    Shirin Najeriya a Yau ya yi fashin bakin kan abin da hukuncin ya kunsa da mataki na gaba ga kanana hukumomi.

    Más Menos
    28 m
  • Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi Cikin Ƙarni Guda
    Jul 11 2024

    Send us a Text Message.

    A wannan makon babban malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman ya samu ni’imar cika shekara 100 a duniya.

    Malamai da mabiya da al’umma sun jinjina yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga Addini.

    Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan gudummuwar da Shehin Malamin ya bayar a cikin shekara fiye da 70 da ya yi yana karantar da Al-Kur’ani.

    Más Menos
    21 m
  • Gaskiyar Magana Kan Bullar Kungiyar Luwadi Da Madigo A Kano
    Jul 9 2024

    Send us a Text Message.

    Labarin bullar wata kungiyar da ake zargin tana rajin yada akidar auren jinsi a Kano na ci gaba da yamusta hazo.

    Tuni hukumomi suka bayyana matakin da za su dauka a kan wadannan zarge-zarge duk da yake sun amince cewa sun taba ganawa da kungiyar.

    Shirin Najeriya a Yau zai bincika yadda aka yi ana zaton wuta a makera, ta tashi a masaka.


    Más Menos
    22 m
  • Dalilin Dawowar Layukan Mai A Najeriya
    Jul 8 2024

    Send us a Text Message.

    Jihohi da dama a wannan lokaci sun fada cikin yanayin dogayen layukan mai da kuma karancinsa.

    Wasu gidajen mai sun kasance a kulle yayin da masu siyarwar kuma farashin sai wanda ya gani, baya ga ‘yan bumburutu da ke cin kasuwarsu a bayan fage.

    Shirin Najeriya a Yau domin jin dalilin wahalar mai a Najeriya

    Más Menos
    27 m
  • Abin Da Ya Sa Ake Ƙara Wa ‘Yan Band A Kuɗin Wutar Lantarki
    Jul 5 2024

    Send us a Text Message.

    Zuwa yanzu masu shan wutar lantarki da ke tsarin Band A sun samu sanarwar kara kudin wutar lantarki

    Sai dai wasu na ganin ba a iya biyan bukatun da wannan kari ba zai samu muhalli ba

    Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne kan Dalilin da ya sa ake kara wa masu tsarin Band A kudin lantarki a kai a kai.

    Más Menos
    18 m
  • Abin Da Dokar Ta-Baci Kan Man Fetur Ke Nufi
    Jul 4 2024

    Send us a Text Message.

    Ana ta musayar ra’ayin bayan da Kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin haƙowa da kuma fitar da ɗanyen mai daga ƙasar.

    Mutane na neman amsar shin me hakan ke nufi, da muhawarar ko hakan abu mai yiwuwa ne?

    Shirin Najeriya a Yau nzai tattauna kan abin da dokar ta baci kan man fetur ke nufi.

    Más Menos
    26 m